in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Afrika kan shige da ficen kayayyaki na hasashen bunkasa kasuwanci a nahiyar da kishi 50 cikin 100 zuwa shekara ta 2032
2012-05-25 15:22:14 cri
Bankin Afrika ya sanar da cewa, kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar ya junansu ta fannin shige da fice na kayyayaki zai karu da kishi 50 cikin 100 zuwa shekara ta 2032, wanda a yanzu ya ke kishi 12 cikin 100, kamar yadda wani jami' in bankin ya sanar a ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban bankin, Denys Denya ya shaidama manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya da cewa, yawancin kasuwanci da kasashen Afirka ke gudana ne tsakanin su da kasashen duniya, kuma wannan lamari na nakasar da nahiyar.

"A matsayin bankin na wata cibiyar kasuwanci da ke kan gaba, muna son yin kokari bunkasa musanya da cinikayya a tsakanin kasashen Afirka zuwa kishi 50 cikin 100 a shekara ta 2032", kamar yadda Denya ya sanar.

Alkalumman kididdiga daga hukumar kasuwanci ta duniya sun nuna cewa, kasuwanci tsakanin kasashen Turai da na Afrika ya kai kishi 65 cikin 100 na dukacin harkokin kasuwanci baki daya na nahiyar, a yayin da sha'anin kasuwanci tsakanin nahiyar Afrika da ta Asiya ya kai kishi 50 cikin 100.

Manyan masu zuba jari a bankin Afirka ta bangaren hada-hadar kusuwanci, sun hada da gwamnatin kasar tarayyar Najeriya, gwamnatin kasar Masar da kuma bankin ci gaban Afrika. Wadannan masu zuba jari a bankin na son yin hulda da bankunan nahiyar Afrika domin gudanar da ayyukan da suka shafi fitar da kayayyaki daga nahiyar zuwa waje.

A cikin shekara ta 2011, bankin ta bada lamunin kudi da suka kai miliyan 500 na dallar Amurka domin gudanar da ayyuka na bunkasa kamfanoni daga tushe a game da fitar da kayyayaki zuwa waje daga cikin kasashen nahiyar Afrika. A yanzu haka dai bankin na da cibiyoyi guda 35 a cikin kasashe 54 na nahiyar, wada kuma ta ke son kara jarinta zuwa biliyan 5 na dallar Amurka zuwa shekara ta 2016. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China