in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Benin na fatan zama wata cibiyar fasahohin sadarwa na zamani na TIC a Afrika
2012-05-25 15:09:10 cri
Gwamnatin kasar Benin na shirin mai da kasar wata cibiyar fasahohin sadarwa na zamani a nahiyar Afrika, a cewar ministan sadarwa na kasar, mista Max Aweke a ranar Alhamis a Cotonou a yayin bikin kaddamar da ayyukan rana ta biyu ta dandalin kasa da kasa karo na bakwai dake maida hankali kan fasahohin zamani na sadarwa da watsa labarai na TIC da ake shigar da su wajen samun cigaba, karantarwa da ba da horo dake dogaro "fadakarwa da samun cigaba mai dorewa".

"A yayin da ya hau kan karagar mulki a cikin wa'adinsa na farko a shekarar 2006, shugaban kasar Benin Boni Yayi, ya sanya wannan mataki a cikin jerin manyan ayyukan gwamnatinsa, musammun ma na mayar da kasar Benin wani sansanin fasahohin sadarwa na zamani a Afrika", in ji minista Max Aweke.

A cewar wannan jami'in siyasa na ma'aikatar sadarwa ta kasar Benin, kan muhimmancin harkokin TIC, gwamnatin Benin ta kebe ma'aikata dake kula da wannan fanni tare da kafa cibiyoyi da tsare tsaren ayyuka kamar misalin cibiyar kula da sabbin fasahohin sardarwa na zamani (AGeNTIC) dake aiki wajen watsa da bunkasa muhajoji da kuma layin internet a cikin kasar baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China