Hukumomin kasar Nijar sun kafa wani kwamitin kasa a ranar Alhamis a Niamey, babban birnin kasar a karkashin jagorancin ministar kasar mai kula da harkokin jama'a, madam Maikibi Kadidiatou Dan Dobi. Kafa wannan kwamiti shi ne na bada kariya da kiyaye zaman rayuwar mutanen da suka tsufa ta hanyar daukar nauyin tsoffin mutane dake cikin tsare tsaren yaki da talauci a cikin kasar Nijar.
A kasar Nijar, a cewar wata kiddidigar al'umma da muhalli ta baya baya, bisa yawan al'ummar kasar dake miliyan 11,6 kusan 496126 wato kimanin kashi 4.48 cikin 100 tsoffin mutane ne dake da shukaru 60 ko fiye da haka a duniya. (Maman Ada)