An kaddamar da taron tattaunawa na shekarar 2012 a ranar 22 Talata 22 ga wata bisa taken "fahimtar juna da yin hadin kai" kuma za a kwashe kwanaki hudu ana yinsa a nan birnin Beijing. Dubban wakilai daga kasashe kimanin 20 na nahiyoyin Asiya, Afrika, Amurka, Euro suke halartar taron domin tattaunawa kan batun yadda za su kara fahimtar juna da habaka hadin kai.
Tsohon shugaban kasar Botswana Festus Mogae wanda ya jima yana kawo ziyara a nan kasar Sin dake halarta, ya ce, ya taba kawo ziyara a kasar Sin a matsayin jami'in gwamnati ko dan siyasa. Abin da ya ba shi damar fahimtar tsarin siyasa da al'adun kasar Sin sannu a hankali, ban da wannan kuma, yana kaunar abincin kasar Sin kwarai da gaske.
Festus Mogae yana son fahimtar kasar Sin ta hanyoyi daban-daban. A ganinsa, ba ma kawai, Sin ta kasance wata muhimmiyar kasa ga kasashen Afrika ta fuskar fitar da kayayyaki, har ma ta kasance mai zuba jari da mai samar da kimiyya da fasaha ga nahiyar Afrika. Ya ce, 'yan kasashen Afrika na da matsayinsu, 'yan kasuwa ba su kasance masu ba da sadaka ba. Muhimmin nauyin da Sin take dauka shi ne, nunawa kasashen Asiya da Afrika cewa, kada su yi dogaro da kasashen yamma sosai.
A ganinsa, a bangaren cinikayya, cinikin kayayyakin da aka sarrafa ya bunkasa sosai, kuma yawansu ya karu. A sa'i daya kuma, kasashe da dama na gudanar da aikin sake sarrafa kayayyaki da dauyen kayayyakin da suke shigo da su sannan kuma su fitar da su. Ya ce, akwai kasashe da yankuna mafi karfi a fannin tattalin arziki kamar su yammacin nahiyar Turai, arewacin Amurka, da kuma kasashe da yankuna masu tasowa da kasashen BRICKS, haka akwai kasashe da yankuna dake samun koma bayan tattalin arziki, musamman ma a wasu kasashen dake nahiyar Afrika. Sin ta kasance kasa ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya, kuma kasa ce mai tasowa. Saboda haka, Sin ta fahimci dukkan kalubalolin da kasashe masu tasowa suke fuskantar. Yana fatan kasar Sin da mahalarta taro na kasashe daban-daban su yi musayar fasahohi masu daraja da alfanu.
Eda Satsuki shugaban majalisar dattijai ta kasar Japan wanda shi ma ya halarci taron ya ce, jigon wasannin Olympics da aka yi a birnin Beijing wato "Duniya daya, buri bai daya" na yin tasiri sosai a duniya, amma, akwai bambancin ra'ayi tsakanin kasashe daban-daban. Ban da hadin kai tsakanin bangarorin Sin da Japan da hadin kai bisa ka'idar MDD, hadin kai tsakanin bangarori daban-daban na da muhimmanci sosai. Alal misali, kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashen Asiya wato ASEAN, kungiyar hadin kai ta tattalin arziki ta Asiya da Pacific, taron shugabannin gabashin Asiya da sauransu, dukkansu sun sa kaimi ga fahimtar juna da hadin kai da ake yi a yankin Asiya da Pacific. Wannan yanki da ma duniya ba za su iya samun zaman wadata, sai idan an tabbatar da zaman lafiya mai karko. Babu wata kasa da za ta iyar samun moriya cikin rikici.
Game da sauyin da kasar Sin take fuskantar. Shugaban ofishin binciken batutuwan kasa da kasa na kasar Sin Qu Xing ya ce, Sin na kokarin kiyaye yanayi wanda zai yi tasiri wajen tabbatar da samun bunkasuwa cikin lumana a duniya. Ya ce, game da rikicin dake barkewa a yammacin Asiya da arewacin Afrika, Sin na nacewa ga ka'idar hana tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata kasar da kokarin warware rikici cikin lumana, sa'i daya kuma, Sin tana lura da matsayin da kungiyoyin AL, AU da dai sauran kungiyoyin yankuna da wasu kasashen Larabawa suke dauka. Sin ta kiyaye wasu manyan ka'idojin kasa da kasa da suka shafi moriyar kasa da dangantakar kasa da kasa yadda ya kamata.Game da kalubalolin da kasashen yamma suke fuskanta, Sin ba ta tsamanin cewa kasashen yamma na lalacewa, maimakon haka, ta jaddada kan kasancewar bangarori masu tasiri da dama a duniya, da kuma hanyoyin samun bunkasuwa da yawa. Tana fatan kowa ya yi hakuri da juna, koyon fasaha daga juna, fitar da wata hanyar samuna jituwa a duniya bisa kokarin gwajin ayyukan da ko wace kasa ke gudanarwa. Yayin da ake tabo batun kalubalen da ake fuskantar a fannin tattalin arziki a duniya, Qu Xing ya ce, Sin ta taka rawa wajen daidaita tsarin tattalin arzikin duniya, sa'i daya kuma, tana yi hadin kai da kasashe daban-daban domin kawo moriyar juna. Game da batun sauyin yanayin da kasar Sin take fuskantar, Sin tana tsayawa tsayin daka kan dogaro bisa karfin kanta da yin hadin kai ta hanyar lumana diplomasiyya, da kuma kokarin karfafa kwarewarta wajen tsaron kai. Ban da wannan kuma, Sin na kara taka rawarta game da makamar al'ummar duniya.
Tsohon firaministan kasar Canada Sheila Copps ta ce, ko wace kasa na da tsarin siyasa, tattalin arziki da al'adunta, kuma na da hanyar da ta samu wajen bunkasa kanta. Ya kamata, mu mutunta hanyar da wata kasa ta zabi tare da kara fahimtar juna, habaka hadin kai da tinkarar kalubale tare, da kuma dauki nauyin dake bisa wuya tare don samun moriyar bai daya.
Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin, kuma shugaban kungiyar yin mu'ammala da kasashe daban-daban ta kasar Sin Zhou Tienong ya yi jawabi a gun bikin kaddamar da taro, inda ya bayyana 'yan hakuri a matsayin babbanr hanyar da za a bi wajen kokarin mumutn ta hanyoyin daban-daban da kasashe suka zaba.(Amina)