Malam Ali Buge Kiragi a jihar Yobe, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Bisa la'akari da yawan taimakon da kasaitaciyar sabuwar kasar Sin ta zamani take bayarwa ga kasashenmu na Africa masu tasowa, muna iya cewa kasar Sin ta zamani tana kara matsa kaimi wajen ingiza zaman lafiya da bunkasa tattalin kasashen nahiyar Africa baki daya. Daga shekarar 1956 da aka kafa huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu tsakanin sabuwar kasaitaciyar kasar Sin ta zamani da kasashenmu na Africa masu tasowa, kawo yanzu 2012 an samu gagarin ci gaba da sakamako mai armashi da inganci da yalwatuwa da moriya mai yawan gaske tsakanin kasar sin da Africa. Har abada kasashenmu na Africa ba za su taba mantawa da dunbun taimako da soyayya da kauna da kasar sin ta nuna wa kasashen Africa. Daga karshe muke kira ga kasar sin da ta kara matsa kaimi sosai wajen tallafawa kasashen Africa kudu da sahara da fusahar noma ta zamani tare da wasu sabbin iri da kuma dabarun noma, domin ceton kasashen yankin daga barazanar kamuwa da yunwa."
Bello Abubakar Malam Gero, shugaban kungiyar masu sauraronmu a jihar Sokoto ta Nijeriya ya aiko mana da sakon cewa, "Ina mai amfani da wannan dama in nuna godiyarmu ga dukkanin ma'aikatan gidan rediyon kasar sin CRI musammam sashen hausa da ma'aikatansa a kan gabatar da gaisuwar ta'aziya da kuka yi na dan uwanmu da Allah yaima cikawa akwanakin baya, a gaskiya wannan yana nuna mana da cewa, wannan gidan rediyon cri na jama'a ne kuma yana da dangantaka mai kyau da masu saurarensa domin kuwa duk lokacin da wani abu na murna ko na bakin ciki ya sami mai sauraron wannan gidan rediyo, to ba shakka idan ya sanar da su, to za su taya shi murna ko kuka, wanna ya nuna karar da cewa kuna kula da hakkin masu sauraronku a ko da yaushe."