Kwanan baya, an ba da labari cewa, a wannan shekara kasar Sin za ta dukufa kan shuka da gabatar da shimkafa mafi inganci da kuma samar da kimiya da na'urori mafi kyau a wannan fanni tare da sa kaimi ga gabatarwa manoma fasahar zamani wajen shuka wannan shimkafa, har da tabbatar da cewa, yawan wannan nau'in shimkafa mafi inganci da za a shuka a wannan shekara zai kai fiye da eka miliyan 8.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, nau'in shimkafa 83 da ma'aikatar aikin gona ta tabbatar da aka shuka domin ba da misali a gundumomi 112 da lambobi 6 na larduna 17 ya kai eka miliyan 7.3 a shekarar 2011 wanda ya kai kashi 24.7 cikin dari bisa yawan shimkafar da aka shuka a kasar Sin. Yawan shimkafa da ake samar a ko wane fadin eka ya kai kg 8745, wanda ya fi na shimkafar da ake amfani da ita yau da kullum yawan kg 1017 wanda ya karu da kashi 13.2 bisa dari.(Amina)