Kasar jamhuriyar Benin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da magungunan jabu
Gwamnatin kasar jumhuriyar Benin ta amince da ta sa hannu kan yarjejeniyar yaki da magungunan jabu,wannan kuma wani salo ne na karfafa yin gwagwarmaya da fataucin magungunan da basu da inganci da ake yi cikin kasar ta Benin. Nicolas Sodabi, babban jami'in kula da sashen magunguna da kuma bincike a ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar , shi ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi a cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua.Ya sanar da cewa, wannan yarjejeniya ta yin yaki da magunguna na jabu, ta kasance ta farko a duniya a kuma nahiyar turai , wadda kuma yanzu ta zama bude ga nahiyar Afrika, domin yin yaki da magungunan jabu. Don neman karfafa hanyoyin dakile ayyukan fataucin mugungunan jabu a cikin kasar Benin , gwamnatin kasar ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya tare da amincewa da ita, kamar yadda Nicolas Sodabi ya jaddada.(Abdou Halilou).
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku