Tsarin MDD domin samun cigaba na PNUD ya taimakawa kasar Nijar da dalar Amurka miliyan 6.1 kwatankwacin kudin Sefa biliyan 3 domin ayyukan karfafa zaman lafiya musammun a arewacin kasar ta Nijar. Wannan taimako za'a amfani da shi wajen karfafa karfin babbar hukumar karfafa zaman lafiya da kuma kwamitin kasa na karbar da sa ido kan makaman da suke shiga kasar ta muguwar hanya, wadanda hukumomi guda biyu na kasa sun kasance wasu dabarun karfafa makomar zaman lafiya a kasar Nijar.
Kasar Nijar dai na fama da matsalolin da suke da nasaba da tashe tashen hankali da rikicin siyasa musammun ma na kasashen Mali da Libiya.
A cewar ministan kasar Amadou Boubacar Cisse, gwamnatin Nijar a gaban wadannan matsaloli ta dauki wasu matakan gaggawa da suka shafi daidaita musammun ma munanan sakamako kan tattalin arzikin kasar ta hanyar aiwatar da dabarun tsaro dana cigaba a yankunan Sahara. (Maman Ada)