Yau Laraba 16 ga wata a nan birnin Beijing, an kira taron manema labaru na dandalin farko na sana'ar da ta shafi musulmai a birnin Lanzhou na kasar Sin, inda mataimakin shugaban birnin Lanzhou Niu Xiangdong ya sanar da cewa, za a kaddamar da wannan dandali daga ran 23 zuwa 24 ga watan Yuni a birnin Lanzhou, a shirin kafa sana'ar samar da kayayyakin da musulmai ke amfani da su a karon farko.
Niu Xiangdong ya ce, wannan sana'a na da makoma mai haske saboda yawan musulmai a duniya ya kai kimanin biliyan daya. Gwamnatin birnin Lanzhou za ta yi amfani da manufofi mai kyau da gwamnatin kasar Sin ta tsara ciki har da manufar raya yankin yammacin kasar Sin da sauransu domin bunkasa sana'ar da ta shafi musulmai ta al'ummar wurin, shigo da kimiyya da ayyuka a wannan fanni da kokarin samar da kayayyakin halal na farko a kasar Sin ta yadda zai zama wani tsari mai inganci dake hada aikin kirkiro, sarrafa, sayarwa waje guda.(Amina)