Bisa labarin da muka samu, an ce, wadannan bukukuwa sama da 20 sun kunshi dandalin tattaunawa tsakanin ministocin al'adu na Sin da Afirka a karo na farko wanda za'a yi a ranar 18 ga watan Yuni a nan birnin Beijing, da bukukuwan kide-kide da raye-raye sama da 10 da za'a shirya a biranen Tianjin, Shanghai, Nanjing, Yinchuan da sauransu, da bukukuwan nune-nune kan kasashen Afirka, da taron karawa juna sani na kasa da kasa kan mutum-mutumi na katako na Afirka da sauransu.
An ce, za'a yi bikin kaddamar da "Mayar da Hankali kan Al'adun Afirka a Shekara ta 2012" a ranar 25 ga wata a babban dakin adana kayan tarihi na kasar Sin dake nan Beijing. Masu shirya bikin sun ce, shirya wadannan bukukuwa, wani muhimmin mataki ne da aka dauka domin cika alkawarin da suka jibanci harkokin al'adu a wajen taron ministoci na dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da Afirka a shekara ta 2009, abun da zai taimaka wajen kara habaka sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka irin ta samun fahimtar juna da cimma moriyar juna ta fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu.(Murtala)