Kakakin hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar Nijeriya ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka sa hannu kan miyagun kwayoyi na cocaine irin na man shafi a kasar Nijeriya. Ya ce, cocaine an sanya ta a cikin wasu kwalaye tamkar kayan abinci da, wani mai sumogar hodar ibilis ya tsuga a cikin firijoji 4 zuwa kasar Nijeriya. Mutumin an taba yanke masu hukunci kan laifin sumogar miyagun kwayoyi kilogiram 1 daga kasar Brazil a shekarar 2010.
Kasar Nijeriya ta kasance wani muhimmin wuri na sumogar din miyagun kwayoyi a yankin yammacin nahiyar Afirka. A wasu shekaru da suka gabata, hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar Nijeriya ta kara yin kokarin wajen yaki da miyagun kwayoyi, da kama miyagun kwayoyi sau da dama a Lagos da sauran tasoshin jiragen sama na kasar.(Zainab)