in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na shirin bunkasa aikin yawon shakatawa ta hanyar kimiyya
2012-05-14 10:34:48 cri

A ranar Lahadin da ta gabata, Marthinus van Schalkwyk, ministan kula da aikin yawon bude ido da shakatawa na kasar Afrika ta Kudu ya furta cewa, kasar za ta bunkasa aikin yawon shakatawa da bude ido domin ganin aikin ya taimaka wajen kawo gudummowa a fannin raya tattalin arzikin kasar mai dorewa. Ministan ya sanar da hakan a lokacin jawabin bude taron nune-nunen lamuran yawon shakatawa na shekara-shekara na nahiyar Afrika mai sunan Indaba.

Ministan ya ce, kamata ya yi a dauki matakai nan da nan ba tare da bata lokaci ba a fannin aikin yawon shakatawa, wadanda za su kawo bunkasar tattalin arzikin da yanzu ake kokarin habakawa, domin kaucewa ayyuka na gajeren lokaci da za su tabarbarar da albarkatun halittunn da ake da su.

Cewar ministan, aikin yawon shakatawa ya kamata ya taimaka wajen tattalin makamashi da raya aikin shakatawa mai dorewa.

Kamar yadda alkaluman kididdiga na baya-baya nan daga gwamnatin kasar suka bayyana, yawan mutanan da suka shigo Afrika ta Kudu daga kasashe daban daban na duniya sun haura miliyan 6.5 a shekara ta 2004 zuwa miliyan 12.25 a halin yanzu, ciki har da wasu miliyan 8.3 sun kasance 'yan yawon shakatawa.(Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China