Ranar Jumma'a 11 ga wata, a yayin da take halartar taron koli kan Afirka na dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa a karo na 22 a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, madam Omobola Johnson, ministar fasahohin sadarwa ta kasar Nijeriya ta ce, kasarta za ta kafa cibiyar bunkasa aikin kirkire-kirkire, a kokarin kara karfafa gwiwar kwararru masu ilmin kirkire-kirkire, ta yadda za su samu nasara a harkokin kasuwanci bisa ga tunaninsu, don kyautata karfin Nijeriya ta fuskar kimiyya da fasaha daga dukkan fannoni.
Ministar ta kara da cewa, cibiyar za ta kasance wani muhimmin sansanin kasa a fannonin nazarin kimiyya da horar da kwararru, wadda kuma za ta bai wa kwararrun taimakon da ya wajaba a fannonin kudi da fasaha. Sa'an nan kuma, ministar ta bayyana fatanta na ganin masana'antun kasar Nijeriya da na kasashen ketare sun zuba jari a kasuwar kasar ta fuskar aikin kirkire-kirkire. (Tasallah)