Shugaban kasar Jamhuriyar Benin, Boni Yayi ya kadamar da taron kammala tsarin yin watsi da yin amfani da magungunan da ba su da inganci. An bude taron ne a ranar Alhamis a birnin Cotonou, domin daidaita tsarin kokowa da wannan annoba. Wannan taro zai taimaka wajen karfafa hanyoyi daban-daban na yin kokowa da yin amfani da magunguna na jabu ta hanyar wayar da kan jama'a a fannoni daban-daban. Shugaban kasar ta Benin ya furta cewa, burin wannan tsari shi ne yin nasara kan kawar da yin amfani da magunguna da ba su da inganci. (Abdou Halilou)