A daidai lokacin da aka bude taron tattalin arzikin duniya kan Afrika a ranar Alhamis a Addis Abeba, babban birnin kasar Habasha, an kaddamar da wani sabon tsarin hulda da ake kira "bude kofar kasashe ta hanyar kirkire-kirkire" mai sunan LIONS@FRICA. Shi dai wannan sabon tsari zai taimaka wajen bunkasa hanyoyi na kirkire-kirkire da ayyuka a cikin kasashen nahiyar Afrika. An kirkiro wannan sabon salo na kirkire-kirkire da taimakon gwamnatin kasar Amurka, da hukumar kasar Amurka mai kula da tallafawa wajen ci gaba ga kasashen duniya, da bankin raya Afrika, kanfanin Microsoft, Nokia, infoDev, DEMO da kuma kungiyar da ake kira"Forum Economique Mondial". (Abdou Halilou)