Nijeriya na da makamashin gas mai yawan gaske, an kimanta cewa, yawansa ya kai kimanin biliyan 187000 cf, abin da ya baiwa Nijeriya damar kasancewa ta matsayi na daya a wannan fanni a Afrika. Gwamnatin Nijeriya na fatan raya tattalin arzikin kasar ta hanyar kara samar da gas tun da wuri, tare da sa kaimi ga fitar da gas irin na salon ruwa zuwa kasashen waje, ta yadda za ta mai da sana'ar gas a matsayin babbar hanyar raya tattalin arzikin duniya.(Amina)