Kafofin watsa labaru na kasar Nijeriya sun ruwaito rahoton kwararru a fannin tattalin arziki na Ingila suka fitar, da ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, yawan kudin da nahiyar Afrika za ta kashe zai kai dalar Amurka biliyan 1500.
Wannan rahoto ya ce, yawan mutanen Afrika zai kai fiye da biliyan 1.5 a cikin shekaru 10 masu zuwa, ya zuwa shekarar 2050, wannan adadi zai kai biliyan 2. Ban da haka kuma, ya zuwa shekarar 2015, matasan da yawan shekarunsu bai kai 15 ba zai kwashe kusan rabin yawan mutanen Afrika, wadanda za su taka muhimmiyar rawa wajen sayen kayayyaki. Kuma sakamakon karuwar yawan mutanen Afrika da karuwar yawan mutanen dake samun matsakaicin albashi, sun bayyana cewa yawan kudin da jama'ar Afrika za su kashe zai karu sosai.(Lami)