in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guardiola ya jagoranci kungiyar Barcelona wajen samun nasarori da yawa
2012-05-09 15:55:48 cri
Za  mu yi bayani kan kungiyar wasan kwallon kafa da ta fi janyo hankalin masu sha'awar wasan kwallon a duniya baki daya a halin yanzu, wato kungiyar Barcelona ta kasar Spain a nahiyar Turai.

Kungiyar nan ce ake cewa ta riga ta kai wani matsayi na 'Universe', wato ana nufin ta fi sauran kungiyoyin dake duniyarmu ta wasan kwallo.Wato ta kai kololowa, daga ita sai kidin tashi in ji malam bahaushe.

Duk da cewa a cikin jerin kungiyoyi mafi karfi a duniya, tana bin Mancester United a matsayi na 2. Amma alkaluma kididdiga sun nuna cewa, kungiyar Barcelona tana da masu goyon baya da suka kai miliyan 270 a duniya.

Gaskiya tana samun karbuwa sosai ga jama'a masu sha'awar yadda ake taba leda. Sai dai ana ganin cewa, kungiyar da ba za ta cimma wani matsayi ba, ba dan namijin kokarin da mai horar da 'yan wasanta Josep Guardiola Sala ya yi ba, wanda kuma ya jagoranci kungiyar wajen samun nasarori da dama.

An ce mutumin yana da da'a da hakuri, kwazo da kuzari, natsuwa da tsari mai kyau a cikin aikin shi na bada horo. Don haka yana kokarin sanya 'yan wasansa su ma sun zama masu biyaya da da'a, wadanda ke girmama ka'idojin kungiyar, ta yadda ya sanya 'yan wasan suka zama tsintsiya madaurinki daya, kuma suka kawar da nuna girman kai.Ka san a kan ce "kowa ya durkusama wada ,sai ya tashi da tsawon shi".

An ce, bayan da Guadiola ya hau kujerar aiki, ya fara bukatar 'yan wasan kungiyar da su ci abinci tare da juna, da fita waje wajen shakatawa tare da juna, da koma wurin zama komina su zauna a tare, har ma ya bukace su da su zama tare da juna a galibin lokacin wata rana da ta kasance ranar zama tare ta mussamman..

Ban da haka, ya sallami wasu fitattun 'yan wasa kamar su Ronaldinho Gaúcho, Samuel Eto'o Fils, Zlatan Ibrahimovic, domin cikinsu akwai wanda ke neman mata fiye da kima a bayyane, da wanda ke son yin magana maras dacewa, wadanda a ganinsa, ba su dace da irin muhallin da yake kokarin samarwa ba a kungiyarsa .

Har ma an ce Guadiola bai yarda da 'yan wasan kungiyar Barcelona da su tuka motoci masu tsada sosai ba irinsu samfurin Porsche da Ferrari da dai makamantansu. Saboda yana ganin cewa mutum mai tawali'u ba zai ci tura ba.

Josep Guardiola Sala, mai horar da 'yan wasan kungiyar ta Barcelona, ya samar da gudunmawa sosai wajen inganta karfin kungiyar, ban da shi kuma bai kamata ba mu manta da wani mutumin da ya yi tasiri sosai shi ma a kungiyar a cikin tarihi , wato Hendrik Johannes Cruijff, tsohon mai horar da 'yan wasan kungiyar, wanda ya kafa makarantar koyar da fasahar taka leda ta La Macia.

Makarantar ta samar da kashi 50% na 'yan wasan kungiyar Barcelona a tarihi. Cikin 'yan wasan kungiyar 20 na yanzu, akwai mutane 9 da suka fito daga makarantar La Macia.

Har ma Guadiola shi kansa ya koyi fasahar buga kwallon kafa a cikin makarantar. Don haka ana kallon yadda dan kasar Holland Hendrik Cruijff ya kafa makarantar La Macia shekaru fiye da 20 da suka gabata a matsayin wani babban dalilin na samar da cikakken horo da ya haifar da wannan fitacciyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona.

Cruijff ya taba magana cewa, nasarorin da Guadiola da kungiyar Barcelona suka samu sun daukaka matsayinsa. Domin duk wani lokacin da aka yi bayani kan fasahar musamman ta kungiyar Barcelona, za a ambaci sunan Cruijff.

Guadiola ya gaji fasahar tiki-taka da Cruijff ya kirkiro, fasahar da ta sanya 'yan wasa ke dinga gudu da buga wa juna kwallo ba tare da tsayawa ba, don neman samun damar buga kwallo cikin gidan abokan karawarsu.

Fasahar da ta sanya kungiyar Barcelona ta kasar Spain shiga cikin jeran kungiyoyi mafi kwarewa a duniya, wacce kuma ta zame wa sauran kungiyoyin kasashe daban daban abin koyi.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China