A cewar Leopol Mboli, ministan makamashi da man fetur na Afrika ta Tsakiya, kasashen biyu na shirin sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin kasuwanci a cikin watanni masu zuwa.
"wadannan shawarwari na samun kulawa mai kyau daga manyan jami'an kasashen biyu", in ji Mboli.
A nasa bangaren, ministan makamshi da man fetur na kasar Cadi, Ibrahim Hileou ya ce, "dangantaka a tsakanin kasashen biyu da kuma tsakanin al'ummomin biyu na cikin yanayi mai kyau ta misalin dunkulewa da hadin kai na Afrika."
Shugaban kasar Cadi Deby Itno ya kai wata ziyarar aiki da zumunci a kasar Afrika ta Tsakiya a ranakun Asabar da Lahadi. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kasashen biyu sun nanata niyyarsu ta karfafa huldar dake tsakaninsu a fannoni da dama musamman ma ta fuskar tsaro, tattalin arziki da kimiyya. (Maman Ada)