A kwanan baya, gwamnatin kasar Zimbabwe ta samu magungunan da hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta taimakawa kasar, wadanda darajansu ta kai dalar Amurka dubu 200 domin yaki da iri-iran cututukan da ake fama da su a yankuna masu zafi.
Bisa labarin da aka bayar, za a ba da wadannan magunguna ne a cikin makarantu da cibiyoyin jiyya na kasar ta Zimbabwe ga mutane miliyan 3.8 dake fama da cututuka irin na yankuna masu zafi, galibinsu yara 'yan kasa da shekaru 15.
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta yi bincike a shekarar 2010 cewa, galibin daliban makarantun firamare da sakandare na kasar, suna dauke da abubuwan da suke haddasa cututuka irin na yankuna masu zafi da rashin kula ke haifarwa. (Lami)