in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya hannu kan wata yarjejeniyar dangantaka game da bunkasa manufofin kawo sauki kan kasuwanci
2012-05-06 17:27:20 cri
Ministan kayayyaki da sufuri na kasar Marocco, kungiyar sufuri ta gamayyar kamfanonin kasar Marocco (FT-CGEM) da kungiyar kasa da kasa kan harkokin sufurin kasa (IRU) sun rattaba hannu a ranar Asabar a birnin Casablanca kan wata yarjejeniyar dangantaka game da bunkasa manufofin kawo sauki kan kasuwanci da sufurin kasa na kayayyaki da mutane a cikin nahiyar Afrika, a cewar wani labari na kamfanin dillancin labarai na MAP.

Bangarorin da suka sanya hannu sun amincewa cimma tsare tsaren hukuma da suka wajaba domin kafa a birnin Casablanca wata tawagar dindindin ta IRU domin nahiyar Afrika da kuma bunkasa tsaron hanyoyi da kuma samun bunkasuwa mai dorewa ta hanyar kafa muhimman ayyukan dake aiki da kwarewa dake cikin hangen kungiyar IRU a nahiyar Afrika.

A cikin takardar wannan yarjejeniya, bangarorin sun dauki niyyar bunkasa kwarewarsu ta aiki bisa musammun ma kan ba da horo mai nagarta da makarantar IRU ta gabatar ta fuskar sufuri da makamnatan haka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China