Zaman taron da babban kwamishinan gwamnatin kasar Benin kan tafiyar da shawarwari tare da taimakon tsarin kasashe kan samun cigaba ya shirya, ya hada musammun ma wakilan makiyaya, manoma, jami'an tsaro, da ma'aikatun yankuna na ofishin ministan noma da tsaron jama'a.
A cewar mista Moise Mensah, babban kwamishinan gwamnatin kasar kan tafiyar da shawarwari, zaman taron na kasa na da manufar kawo sauki ga kafa wani tsarin tattaunawa tsakanin bangarori daban daban da abun ya shafa domin samar da wani yanayi mai kyau a wannan fanni, da farko domin moriyarsu sannan kuma domin moriyar cigaban yankuna da kasar baki daya.
Mista Mensah ya nuna cewa, rashin issasun kayayyakin aiki na zamani a nahiyar Afirka na kawo matsala, kuma ana da nisa wajen gudanar da irin kiwo na zamani.
"dalilin haka, garke-garken shanu da kananan dabbobi suke fita waje domin su yi kiwo. A cikin wannan tafiya tasu su kan take shuke-shuke ko kuma su mayar da gonaki wani wurin kiwonsu, su lalata kokarin da manoma suka yi na tsawon watanni, wanda matsalar za ta hana su samu albarkatun noma", in ji jami'in. Sannan ya kara da cewa, "da a ce dokoki da matakai da aka cimma suna aiki, to da sana'ar za ta taimakawa manoma da makiyaya".(Maman Ada)