in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Benin ta sake dokar gudanar da lamuran auduga
2012-05-01 15:07:24 cri
Gwamnatin kasar Benin ta kuduri dokar gudanar da lamuran bangaren kada ko kuma auduga da kanta, bangare ne da take ba da tallafi na biliyoyin kudin sefa, a sheraru da dama da suka gabata. Gwamnatin ta yi hakan ne sabili da rashin samun sakamako nagari a bangaren noman kada, tare da tsammanin cewa, an handame kudin da take zubawa na tallafi a wannan bangare. Abun da ya jawo aka tsare wasu jami'ai masu kula da bangaren kada na kasar a cikin satin da ya gabata, kamar yadda wata sanarwar da bangaren gwamnatin kasar ta Benin ta sanar a ranar Litinin 30 ga watan Afrilu. Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin ta dauki matakin dakatar da kudurin da ta dauka a shekara ta 1999 mai ba da damar samun irin shukka ga manoma.

Gwamnatin za ta girka wani kwamiti na kasa da firaminista zai jagora, wanda kuma zai kula da sa ido kan bangaren lamuran kada. Haka kuma gwamnatin da kanta za ta kula da abun da ya shafi ba da irin kada ga kankana da manyan cibiyoyi na ma'aikatun kula da noma, kiwo da su wato kamun kifi, ta hanyar ma'aikatun gundumomi, magadan gari da kuma soji, a cewar sanarwar. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China