in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya za ta bunkasa noman shimkafa
2012-05-01 15:06:42 cri
Gwamnatin jihar Imo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya ta dauki aniyar noman shimkafa mai yawa a cikin tsarinta na bunkasa harkar noma.

Gwamnan jihar Rochas Okorocha shi ya sanar da hakan a garin Owerri, inda ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta soma tattaunawa da kwararrun da suka fito daga kasar Thailand domin soma aikin noman shimkafa mai yawa a cikin jihar.

Gwamnatin jihar ta Imo za ta girka wani kamfanin samar da shimkafa domin amfanin jama'ar wurin, da kuma sayarwa, kamar yadda mista Okorocha ya sanar.

Wannan yarjejeniya za ta tabbatar da samar da guraban aikin yi da kuma bunkasa bangaren noma, kamar yadda jami'in jaddada. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China