An labarta cewa, a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, Foumakoye Gado, ministan makamashi da man fetur na Nijer ya rattaba hannu kan yarjejeniyar kungiyar APPA da abin ya shafa.
An kafa kungiyar APPA a ran 27 ga watan Janairu na shekarar 1987, wadda ta kafa babban zaurenta a kasar Congo(Brazzaville). Yanzu kungiyar tana kunshe da mambobi guda 18, kamar kasashen Afirka ta Kudu, Masar, Algeria, Angola, Kamaru da dai sauransu. Kana kuma, yawan danyen man fetur da kasashen kungiyar suke fitarwa a ko wace rana ya wuce ganguna miliyan 9 da dubu dari 8.(Tasallah)