Ya sanar da hakan ne a lokacin bude taron mahawara hukumar FAO kan yankin Afrika karo na 27, mahawarar da za ta duba hanyoyin da suka dace domin bunkasa aikin noma a nahiyar Afrika sabili da rage gibin kalaci da ake samu a nahiyar.
Nahiyar Afrika na kashe sama da biliyan 50 na dallar Amurka domin shigo da kalaci daga waje. Ta wani bangare kuma a lokaci guda, kishi 50 cikin 100 na ma'aikatan nahiyar sun kasance a cikin kananan rukunoni na manoma, makiyaya, masu kula da gandun daji da kuma masunta, da ke kokarin ganin cewa, sun kawo gudummowa domin nahiyar Afrika ta ciyar da kanta, kamar yadda ya sanar a wannan taro.
M. Graziano ya sanar da cewa, aikin noma a nahiyar Afrika na cikin wani lokaci na canji mai fa'ida da kuma ke da bukatar sabbin mataimaka da kuma sabbin dabaru da tsinkaye.
Ya kara da cewa, ya kamata mu taimaka wa manoman Afrika, domin su samar da kalaci mai dama, kuma domin wajen samar da kalacin ya kasance cikin hanya mai nagarta, sabili da rubanya yawan kalacin da za su samu, kuma ya wadatar da jama'a, ganin yadda yawan bukatar kalaci ke karuwa a nahiyar. Ya sanar da hakan ne ga dimbin masu fada a ji da kuma masu daukar matakai ta bangaren aikin noma da ke halartar wannan muhawara. (Abdou Halilou).