Sidibe ya sanar da hakan ne a lokacin da ya ke jagorantar tawagar jami'in UNAIDS a zauren majalisar dokokin kasar a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata tare da Patience Jonathan uwargidan shugaban kasar Najeriya, da nufin tattaunawar kawar da kwayoyin cuta a dukkan duniya.
Ya yi kira da cewa, yana son ci gaba da samarwa Najeriya da ma Afrika baki daya ta hanyar matan gwamnoni, hanyoyin kare jarirai daga kamuwa da kwayoyin cutar HIV a cikin kasashen, za a kara fasalin kudi domin tabbatar da cewa an samu cibiyoyin kiwon lafiya na tushe masu inganci domin mata masu juna biyu su rika samun kulawa mai kyau.
Matar shugaban kasar Najeriya, a cikin kalamanta bayan taro game da cutar AIDS ko kuma SIDA a cikin watan June na shekara ta 2011, ta girka kwamiti wanda Ministan harkokin gida na kasa Mohammed Pate ke jagorenta, wanda kuma ke gudanar da aiki kan rahoton da aka bashi. (Abdou Halilou).