Wannan mahawara za ta bada dama ga dubun wakilai daga fannonin aiki da yin amfani da kade, daga Afrika da kuma kasashen duniya, musamman daga bangaren masu sarrafa shi zuwa dillalai, daga masu saye zuwa masu sayarwa na kasa da kasa a kasuwanni, da masu sufurin shi, masu zuba jari da masu kula da ingancinsa, masu jigilarsa da dai sauransu, da su tattauna kan hanyoyin girka kamfanoni sarrafa kade, Kamar yadda ministar kula da kamfanoni da kasuwanci, kanana da matsaikatan masa'anantu ta kasar jamhuriyar Benin ta sanar.
Ya furta cewa, wannan taro zai sanya masu hidima ta fannin kade na Afrika da na kasashen duniya, su kula da dangantakar kasuwanci, da samar da sassa daban-daban a bangarori da dama kan harkar kade.
Ministan kare muhalli na kasar Burkina Faso, ya sanar da cewa, kade na da muhinmanci a cikin rayuwar al'ummar karkara.Ya kasance kalaci, kuma hanyar samun kudi, hanyar samar da aiki ga jama'a. Ana amfani da shi wajen sarrafa maganin gargajiya, magungunna na zamani da kuma kayan shafe-shafe na gyara jiki.
Daga shekara ta 2005 kasashen Yammacin Afrika sun zuba miliyoyin kudi na dalar Amurka domin samar da ayyukan yi ta fannin kade.(Abdou Halilou).