Kwanan baya, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya gabatar da ka'idojinsa na gudanar da mulkin kasa, inda ya nuna cewa, kasar ta yi shirin samar da guraben aikin yi dubu 500 ta hanyar raya sana'ar kamun kifi kafin shekarar 2015.
Ya zuwa yanzu, yawan abinci da kasar ta shigo da shi na karuwa da kashi 11 bisa 100 a ko wace shekara, daga cikinsu yawan kudin da aka kashe a fannin shigo da kayayyaki game da sana'ar kamun kifi ya kai dala biliyan 8.125. Ban da wannan kuma, Goodluck Jonathan na fatan rage yawan kudi da za a kashe wajen shigo da abinci zuwa dala miliyan 600 ta wannan shiri.
A halin yanzu, yawan kifaye da ake samarwa a ko wace shekara a kasar Nijeriya ya kai ton 1240, kuma yawan mutane da wannan sana'ar ta shafa ya kai miliyan 6.(Amina)