Kamfanin kasar Sin da ke watsa shirye-shiryen talibijin a Nijeriya wato kamfanin Startimes, wanda ya shiga cikin kasuwar Nijeriya ba da dadewa ba, ya samu karbuwa matuka, sakamakon shirye-shirye masu inganci, ban sha'awa da kuma araha da ya ke watsawa, musamman ma wasu shirye-shirye cikin harshen Sinanci, domin haka galibin Sinawa da ke Nijeriya suna sha'awar kallon wadannan shirye-shiryen.
Daya daga cikin kamfanonin da ke takara da kamfanin Startimes shi ne DSTV daga kasar Afrika ta kudu. hakika, akwai masu kallon DSTV da yawa a Nijeriya, sannan ya ji tasirin takarar da suke da kamfanin kasar Sin, wannan ya sa ya aiwatar da wasu gyara kan shirye-shiryensa, wato daga wannan shekara da muke ciki, ya fara watsa shirye-shirye cikin harshen Sinanci, domin jawo hankulan masu mu'amula da kamfanin Startimes.(Danladi)