in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afrika ta kudu na kira ga al'ummar kasar da su taimaka mata wajen gwagwarmaya da farautar dorinar daji
2012-04-22 19:33:51 cri
A ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta yi kira ga al'ummar kasar da su taimaka mata wajen yakar masu farautar dorinar daji, ganin cewa yawan dorinar dajin da ake halakawa ba cikin ka'ida ba na karuwa.

A cikin wata sanarwa da hukumar kula da harkokin muhalli ya bayar, an ce, "a yau, an halaka dorinar daji 18, akwai fargaba a game da lamarin."

Hukumar ta kuma nuna cewa, gandun dajin kasar na Kruger ya yi hasarar dorinar daji 111 da aka kashe ba cikin ka'ida ba tun farkon shekara zuwa yanzu.

An halaka dorinar daji guda 25 ba cikin ka'ida ba a Limpopo, guda 18 a Kwazulu-Natal da kuma 17 a yankin arewa maso yammacin kasar, wasu guda 10 na daban a cikin yankuna daban-daban na kasar.

Sanarwar ta nuna cewa, an samu ci gaba ta hanyar cafke maharba masu taka doka guda 113.

A shekarar bara maharba masu taka doka guda 232 ne aka cafke a kasar Afrika ta Kudu, a yayin da guda 26 suka mutu a cikin kwashi ba dadi da hukumomin tsaron gandun daji. A cikin shekara ta 2010 maharba masu taka doka guda 165 ne aka cafke.

Duk da yawan furofagandar da ake yi a kai a kai ga jama'a kan illar yin farautar dorinar daji ba cikin ka'ida ba, ba ta sa aka samu raguwar yawan dorinar dajin da ake halakawa ba. A shekarar da ta gabata, dorinar daji 448 ne aka halaka a kasar Afrika ta kudu, daga cikinsu guda 19 babaku ne, irin launin da ke fuskantar bacewa, wadanda a halin yanzu yawansu ya kai kasa da 5000 a daji.

Sama da kashi 34 cikin 100 a shekara ta 2010, wato kimanin dorinar daji 333 ne aka kashe, kusan sun lumka sau 4 wadanda aka kashe a shekara ta 2009 da yawansu ya kai 122.

Ana tuhumar wasu kungiyoyi na kasa da kasa da kasancewa da hannu a cikin wannan lamari na halaka dorinar daji ba cikin ka'ida ba.(Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China