Manyan jami'ai masu kula da kiwon lafiya na kasashe guda 15 mambobin kungiyar na halartar taron domin tautaunawa kan maganar kiwon lafiya da ke cikin shirin bunkasuwa na MDGs da MDD ta tsara a shekara ta 2000.
Yankin yammacin Afrika na fuskantar matsalolin kiwon lafiya, kamar rashin sukunin zuwa asibiti da al'umma ke fuskanta sakamakon talaucin da jama'a suke da shi, abun da ya kawo matsalar samun magani yadda ya dace, kuma babu asibitoci masu inganci. Mahalarta taron za su tattauna kan manufar bai daya a cikin yankin ta bangaren kiwon lafiya.
Har wa yau karfafa samar da ma'aikatan kiwon lafiya zai kasance wani abu mai muhimmanci da mahalarta taron za su yi magana a kai.
A yayin da ake gudanar da wannan taro, shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya shirya liyafa ga ministocin kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS, inda ya tausaya a game da yanayin da kasashen Afrika suke ciki a bangaren kiwon lafiya. (Abdou Halilou)