Ma'aikatar ta sanar da cewa, an rufe kamfanonin guda 2 da suka hada da kamfanin Akintola-Williams da kamfanin Adekanola bayan da 'yan majalisar wakilan kasar suka gano cewa, kamfanonin na da hannu dumu-dumu a cikin lamarin zamba a kan kudin tallafi ga mai.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar ta girka wani kwamiti da zai diba koken da jama'ar da lamarin zambar ya rutsa da su, suna kuma neman samun diyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu labari daga ma'aikatar kudi ta kasar Nijeriya.
Majiyoyin da ke da masaniya sun ce, kwamitin zai tabbatar da cewa, mutanen da lamarin zambar ya shafa sun yi koke ne bisa ka'ida.(Abdou Halilou)