Dabarar kasar ta Nijar mai sunan 3N an kirkiro ta ne domin yi gwagwarmaya da matsalar kalaci, kuma wata dabara ce ta samar da kalaci da samar da ci gaba mai dorewa ta bangaren aikin noma, kamar yadda bangaren gwamnatin kasar ta sanar.
Wannan dabara za ta maye gurbin sauran dabarun da suka gabata ta bangaren bunkasa ayyukan noma da samar da kalaci ta hanyar yin la'akari da darussan da aka samu a baya da kuma ayyuka na gari da su ka gudana, kamar yadda sanarwa ta jaddada.
Dabarar 3N za ta taimakawa a matsayin wani ginshiki a game da dukkan wani tsari ta fannin bunkasa bangaren noma da samar da kalaci, da samun koshi da abinci mai gina jiki a yankunan birane da na karkara.
Kamar yadda taron majalisar ministoci ta sanar, an kiyasta cewa, wannan tsari na bukatar kudin da su ka kai biliyan 1 da miliyan dari 8 da 15 na dallar kudi sefa.(Abdou Halilou)