Kasar Sudan ta kudu ta shiga asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da kungiyar bankin duniya a ran 18 ga wata, wannan ya sa yanzu ta zama sabon memban wadannan kungiyoyi biyu na duniya.
Shugabar asusun IMF Christine Legarde ta bayar da sanarwa cewa, kasar Sudan ta kudu na fuskantar kalubale da dama, asusun IMF zai yi iyakacin kokarin taimakawa kasar wajen aza harsashi ta yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar a nan gaba.
A wannan rana, mataimakin shugaban bankin duniya mai kula da harkokin Afrika ya bayyana cewa, bankin duniya zai dukufa kan taimakawa kasar Sudan ta kudu wajen inganta rayuwa da tattalin arzikin al'ummar Sudan yadda ya kamata.(Lami)