Babban darektan hukumar dake kula zirga-zirgar jiragen saman fararen hula ta NCCA, Harold Demuren ya yi wannan sanarwa a birnin Abuja, inda ya bayyana cewa, sabbin matakan za su taimakawa hukumar yanke hukunci ga duk wani kamfanin jiragen sama na cikin gida ko na waje da zai soke ko kawo jinkiri kan zirga-zirgar jiragen samansa ba tare da wani dalili ba.
Haka kuma za'a sanya allunan bada bayanai na zamani a cikin filayen jiragen saman kasar domin baiwa fasinjoji damar samun karin haske game da tafiye-tafiyensu.
Shugaban NCAA ya nuna cewa, allunan bada bayanai na zamani zasu taimakawa fasinjoji samun kayayyakinsu da suka bace, tare da nuna musu inda kuma zasu iya ajiye kararraki game da wasu matsalolin kamfanonin jiragen saman.
Haka zalika mista Demuren ya bayyana cewa, hukumarsa zata yin hadin gwiwa tare da hukumar tarayya ta filayen jiragen saman kasar Najeriya (FAAN) domin sa ido kan cewa duk filayen jiragen sama suna amfani da wadannan matakai da zasu taimakawa fasinjoji samun 'yancin zuwa kowane filin jiragen saman dake cikin kasar. (Maman Ada)