in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu mafari mai kyau a tattalin arzikinta na bana
2012-04-03 20:57:45 cri
A Talata 3 ga wata, a gun taron dandalin tattaunawar harkokin Asiya da aka yi a birnin Bo'ao da ke kudancin kasar Sin, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin, Mr.Zhang Xiaoqiang ya ce, bisa ga kwarya-kwaryar alkaluman da sassan da abin ya shafa suka bayar, an ce, yawan GDP ya karu da kimanin kashi 8.4% a kasar Sin cikin farkon watanni uku na bana, a yayin da ma'aunin da aka sani da CPI kan farashin kayayyakin da mazauna birane ke saya ya karu da kimanin kashi 3.5%, abin da ya shaida wani mafari mai kyau ga tattalin arzikin kasar a wannan shekara.

Mr.Zhang Xiaoqiang ya fadi haka ne a gun wani taron tattaunawa kan makomar tattalin arzikin duniya a shekarar 2012, inda ya waiwayi burin da gwamnatin kasar Sin ke neman cimmawa a rahoton aikin da ta gabatar, inda aka ce, za a yi kokarin tabbatar da yawan karuwar GDP da kashi 7.5%, tare da kayyade karuwar CPI da wajen kashi 4%.

Mr.Zhang Xiaoqiang ya ce, a bana, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin kudi masu inganci, tare da yin kokarin daidaitawa tsakanin karuwar tattalin arziki, gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da kuma kayyade farashin kayayyaki, haka kuma za ta ci gaba da kokarin habaka bukatun cikin gida.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China