in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin kula da yanayi na Sin sun gudanar da ayyuka iri-iri domin tunawa da ranar hasashen yanayin ta duniya
2012-03-18 17:26:18 cri
Ranar 23 ga wata, rana ce ta yanayin duniya. Taken ranar a shekarar bana shi ne "Yanayi da ruwa za su kara kuzari a nan gaba". Don haka, hukumomin kula da harkokin yanayi na matakai daban daban na kasar Sin za su gudanar da ayyukan tunawa, da gabatarwa, da yada ilmin kimiyya iri iri a tsakiya da karshen wannan wata, domin kara fadakar da al'umma kan harkokin yanayi, da kara bayyana ayyukan da hukumomin yanayi ke gudanarwa ta fannonin yin rigakafi da ragen bala'u iri iri, tinkarar sauyawar yanayi, da amfani da ruwan sama da sauransu, ta yadda jama'a za su kara samun fahimta da nuna goyon baya ga ayyukan hasashen yanayi. Hakan zai ba da gudummawa wajen kara karfin jama'a na amfani da hasashen yanayi, ba da tabbaci da kyautata rayuwar jama'a, da kuma sa kaimi ga ci gaban zamantakewar al'umma.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China