in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin daidaita matsalar yaran dake kauyuka da mahaifansu ke zuwa birane neman aiki
2012-03-15 14:05:59 cri

Yao Wenli tana da shekaru goma a duniya, kuma daliba ce dake aji na uku a makarantar firamare ta Yaohe a gundumar Tongwei dake lardin Gansu a kasar Sin, mahaifanta biyu suna aiki a waje, ita kanta tana zauna a kauye tare da kakarta wato uwar babanta mai shekaru sama da tamanin da haihuwa. Yao Wenli ta gaya wa wakilinmu cewa, ko wace rana, tana begen iyayenta sosai. A makarantar firamaren da Yao Wenli da take karatu, kusan rabin dalibai suna cikin irin wannan halin da take ciki, wato mahaifansu su ma sun kaura zuwa birane domin aiki, amma ba tare da su ba.

Dangane da haka, mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma shehun malama ta jami'ar horas da malamai Tang Sulan wadda ke yin nazari cikin dogon lokaci kan batun yara a kauyuka ba tare da mahaifansu ba ta nuna cewa,  "Yanzu a kasar Sin, gaba daya akwai yaran kauyuka da mahaifansu suke zuwa birane domin aiki da yawansu ya kai miliyan 58, a ciki, wadanda ba su kai shekaru 14 da haihuwa ba sun kai miliyan 40, hakika, wadannan yara sun fi bukatar kulawar mahaifa. Kuma yawancinsu suna zaune ne a wararen dake fama da talauci, musamman ma a tsakiyar kasar Sin da kuma yammacin kasar."

Bisa sakamakon binciken da aka samu, an ce, yara a kauyuka wadanda ba su zaman rayuwa tare da mahaifansu su kan gamu da matsala wajen yanayin tunani, wato su kan kasance cikin halin zulumi, hankalinsu ya kan tashi, kuma su kan kasa kula da sauran mutane.

Mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma mataimakiyar direktan kwamitin kula da harkokin yara na kasar Sin Tian Shulan tana ganin cewa, ya kamata yara su yi zaman rayuwa tare da mahaifansu, bai kamata ba su yi zaman rayuwa da sauran mutane da ba mahaifansu ba. Ta ce,  "Idan mahaifan yara sun samu aikin yi a birane, to, ya fi kyau kamfanonin da suke aiki a ciki su yi kokarin samar da sharudan da suka wajaba domin karbar yaransu, da haka, yara za su iya yin zaman rayuwa tare da mahaifansu yadda ya kamata."

Abu mai faranta rai shi ne kafin shekarun da suka gabata, ma'aikatar kula da aikin ba da ilmi ta kasar Sin ta tanada cewa, dole ne makarantun birane su karbi yaran ma'aikatan da suka zo daga sauran wurare domin su yi karata a ciki ba tare da biyan kudi ba. Game da wannan, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma mataimakin magajin birnin Qingdao na lardin Shandong Wang Xiulin ya bayyana cewa, a birnin Qingdao, yaran ma'aikatan da suka zo daga sauran wurare suna iya yin karatu a daukacin makarantu na birnin tare da yaran da aka haife su a wurin kuma ba tare da biyan kudi ba. Wang Xiulin ya ce,  "Kawo yanzu, an kimanta cewa, dalibai da yawansu ya kai kashi 30 cikin dari dake cikin makarantun firamare da na midil yaran ma'aikatan da suka zo birnin domin aiki ne. Kuma muna kokarin kara samar da damar shiga dakunan reno ga kananan yaran ma'aikatan da suka zo daga sauraren wurare."

Hakika, a ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana kokarin cimma burin kyautata zaman rayuwar daukacin jama'ar kasar, musamman ma na yara saboda su ne makomarmu. A dalilin haka, gwamnatin kasar ta kara mai da hankali kan wannan batun, ko da yake, yanzu, wannan matsala ta yi tsanani sakamakon yawansu wato miliyan 58 ke nan, ana fatan za a daidaita matsalar cikin gajeren lokaci yadda ya kamata karkashin kokarin da ake gudanarwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China