in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2012-03-14 16:04:40 cri

A ran 14 ga wata a nan birnin Beijing, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11. Hu Jintao, Wu Bangguo, Wen Jiabao, Jia Qinglin, Li Changchun, Xi Jinping da sauran shugabannin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na gwamnatin kasar sun halarci bikin rufewa.

A gun taron, an zartas da kuduri game da rahoton aikin gwamnatin kasar, da halin da ake ciki yayin da aka gudanar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a shekarar 2011, da kudurin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma na shekarar 2012, da kudurin gyara dokar sauraron karar manyan laifuka da majalisar wakilan jama'ar kasar ta tsara, da kudurin da ya shafi yadda za a yi zaben wakilan majalisar jama'ar kasar, da kudurin da ya shafi rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar, da rahoton ayyukan kotun koli da na hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin da dai sauransu.

A gun bikin rufe taron, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya yi wani jawabi, inda ya nuna cewa, akwai sauran shekara daya a wa'adin majalisar a wannan karo. A shekaru 4 da suka gabata, majalisar da zaunannen kwamitin majalisar sun gudanar da ayyuka bisa doka, da yin kokarin kyautata tsarin dokoki na gurguzu mai alamar kasar Sin, da sa kaimi ga gudanar da manufofin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminits ta kasar Sin ya tsara, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin gurguzu da bunkasuwar zamantakewar al'ummar kasar Sin.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China