in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta karkata ga duk wani bangare kan batun kasar Syria ba
2012-03-14 13:58:36 cri

A ranar 14 ga wannan wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta fi karkata ne ga duk wani bangare kan batun kasar Syria ba, har ma ga gwamnatin kasar Syria.

Wen Jiabao ya bayyana hakan a gun taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a wannan rana. Ya ce, kasar Sin tana da ra'ayoyi 4 game da batun kasar Syria. Na farko, kamata ya yi a tabbatar da tsaron fararen hula, inda aka bukaci bangarori daban daban na kasar Syria da su dakatar da kashe fararen hula nan da nan. Na biyu, Sin ta girmama bukatun jama'ar kasar Syria na neman yin kwaskwarima da tabbatar da hakkinsu. Na uku, Sin ta nuna goyon baya ga manzon musamman na MDD da na kungiyar kawancen kasashen Larabawa mai aikin shiga-tsakani kan wannan batu. Na hudu, Sin ta nuna bakin ciki ga rikicin jin kai da jama'ar kasar Syria suke ciki, kana za ta ci gaba da kokarin ba da taimakon jin kai tare da sauran kasashen duniya.

Ban da wannan kuma, Wen Jiabao ya bayyana cewa, Sin tana gaggauta shiga tsakanin bangarori daban daban na kasar Syria don kaddamar da yin shawarwari ta hanyar siyasa.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China