in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::

Ya kamata a yi kokarin daidaita cinikayyar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, ta hanyar hadin kai, in ji firaministan kasar Sin
2012-03-14 11:47:24 cri
Safiyar yau Laraba 14 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya ce, ya kamata, a warware batun rashin daidaituwa tsakanin kasashen Sin da Amurka da dai sauran matsaloli ta fuskar cinikayya ta hanyar yin hadin kai a tsakaninsu.

Mista Wen ya yi wannan furuci ne a yayin taron manema labaru albarkacin zaman taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 a nan birnin Beijing, haka kuma firaministan kasar ya nuna cewa, ana bukatar bunkasa cinikayyar shige da fice tsakanin kasashen Sin da Amurka domin sa kaimi ga hadin kai da kasashen biyu suke yi a fannin ciniki da zuba jari. Wato a bari, kasar Sin ta kara shigo da kayayyaki daga kasar Amurka yayin da Amurka ta kara fitar da kayayyakinta zuwa kasar Sin tare da kawar da kayyadewa a wannan fanni. Kana ya kamata bangarorin 2 su kara zubawa juna jari. Ya kamata, kasashen biyu su samar da muhalli mai kyau wajen zuba jari tare da ba da tallafi a wannan fanni. Haka zalika, ya kamata, kasashen biyu su kara yin hadin kai a fannonin yin amfani da sabbin makamashi, sabbin kayayyaki, yin tsimin makamashi, zirga-zirgar jiragen sama da ta kumbuna da sauransu, da kuma zurfafa hadin kai ta fuskar gina manyan gine-ginen more rayuwa, sa'an nan su yi kokarin alakanta aikin da hadin gwiwarsu a bangaren aikin kudi.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China