in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Makiyaya a jihar Tibet sun shiga gidajen kwanan da gwamnatin kasar Sin ta samar musu
2012-03-13 15:20:52 cri

Makiyayi Gogo ya fito ne daga kauyen Nalong na garin Wuma na gundumar Dangxiong dake jihar Tibet ta kasar Sin, ya gaya wa wakilinmu cewa, da, makiyaya su kan zauna cikin tantuna dake kusa da ruwa da ciyawa, yara ba su iya zuwa makaranta, kuma tsofaffi ba su iya ganin likita cikin lokaci. Gogo ya ce,  "Da, mun zauna cikin tantuna, in iska ta bushe, ko ina akwai rairayi, ba tsabta, amma yanzu, yanayin ya canja, mun shiga sabbin gidajen kwanan da gwamnatin kasar Sin ta samar musu. An gina wannan gidan kwana da nake zauna a shekarar 2007, fadinsa ya kai muraba'in mita 256, gwamnatin kasar ta ba ni kudin taimakon da yawansa ya kai kudin Sin Renminbi dubu ashirin tare da rancen kudi dubu talatin ba tare da biyan kudin ruwa ba."

Domin kyautata zaman rayuwar makiyaya a jihar Tibet, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da ta jihar Tibet mai cin gashin kanta sun mai da hankali sosai kan aikin. A shekarar 2006, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta zuba jarin da yawansa ya kai kudin Sin Renminbi biliyan 17 a jihar Tibet domin kyautata ingancin zaman rayuwar makiyaya a jihar.

Dangane da haka, wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Bandan Cuomu, 'yar kabilar Menba ce da ta zo daga jihar Tibet ta nuna cewa,  "Tun bayan da aka fara gudanar da aikin taimakawa makiyaya a jihar Tibet domin samun gidajen kwana yadda ya kamata, daukacin makiyaya da yawansu ya kai 685 daga iyalai 253 a garina sun shiga sabbin gidajen kwana. Ban da wannan kuma, hanyoyin wuraren su ma sun samu kyautatuwa a bayyane, kowa da kowa na shan ruwan famfo mai tsabta a cikin gidajen kwanansu. Gaskiya muna jin dadin zaman rayuwarmu."

Mun samu labari cewa, a jihar Tibet, gaba daya iyalai sama da dubu dari uku wato makiyaya fiye da miliyan daya da dubu dari hudu sun samu moriya daga wannan babban aikin samar da gidajen kwana. A shekarar 2011, makiyayan da yawansu ya kai dubu dari uku da arba'in sun kaura zuwa sabbin gidajen kwanan da aka gina karkashin taimakon gwamnatin kasar. A sa'i daya kuma, tattalin arzikin jihar shi ma ya samu bunkasuwa cikin sauri sakamakon kyautatuwar sharudan zaman rayuwar makiyaya.

Yayin da gwamnatin kasar ke ba da himma kan aikin samar da gidajen kwana ga makiyaya, a sa'i daya kuma, tana kokarin kyautata zaman rayuwar makiyaya a sauran fannoni kamar su samar da ruwa, lantarki, hanyoyin mota, sadarwa, talibijin da sauransu. Kan wannan batu, shugaban gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta a kasar Sin Baima Chinlie ya bayyana cewa,  "Wadannan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun taimaka sosai wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar jihar Tibet, alal misali, manoma da makiyaya da yawansu ya kai dubu ashirin da malamai da dalibai dake cikin makarantu da yawansu ya kai dubu 23 sun samu ruwan sha mai tsabta, kuma jama'ar jihar da yawansu ya kai dubu 89 sun fara amfani da lantarki da ake samarwa. An gina hanyoyin mota a yawancin kauyuka a jihar har sun kai kashi 86.4 cikin dari. Ban da wannan kuma, makiyaya a wuraren kashi 65 cikin dari a jihar suna amfani da wayar salula yadda ya kamata. Hakan ba ma kawai ya kyautata zaman rayuwarsu ba, har ma ya kara karfafa cudanyar dake tsakanin mazauna jihar da na sauran wurare na kasar Sin har na duk duniya baki daya."

A shekarar bana, gwamnatin jihar Tibet za ta kara zuba jarin da yawansa zai kai kudin Sin Renminbi biliyan 17 kan aikin domin samar da gidajen kwana masu inganci ga makiyaya na iyalai dubu 185 da dari biyar da suke zaune a tantuna yanzu haka a cikin shekaru uku masu zuwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China