in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron shekara-shekara na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin
2012-03-13 10:16:25 cri

A ran 13 ga wata da safe a nan birnin Beijing, aka kammala taron 5 na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11. Hu Jintao, Wu Bangguo, Wen Jiabao, Jia Qinglin, Li Changchun, Xi Jinping da sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis da gwamnatin kasar Sin sun halarci bikin rufewa.

Shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya shugabanci bikin rufe taron, inda ya yi wani jawabi da cewa, a gun taron, membobin majalisar sun tattauna kan rahoton da gwamnatin kasar ta yi, da bada shawarwari kan yadda za a kyautata manufofi daga manyan fannoni, da gaggauta canja hanyar inganta tattalin arziki, da tabbatar da zaman rayuwar jama'a, da kara bude kofa da yin kwaskwarima da dai sauransu. Membobin majalisar sun bada rahotanni 833, da gabatar da shirye-shirye 6069, da bada labarai 1341 game da halin zamantakewar al'umma da zaman rayuwar jama'a, hakan na bayyana cewa, membobin sun yi kokari sosai domin bautawa kasar da jama'arta.

A gun rufe taron, membobi 2121 na majalisar masu halartar taron sun zartas da rahoton da zaunannen kwamitin majalisar ya yi, da rahoton da aka bayar kan yadda aka duba shirye-shirye, da kuma kudurin siyasa da aka tsara kan wannan taro.

Majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, majalisar koli ce ta bada shawara a kasar, a kan canja membobin majalisar a shekaru biyar biyar, taro shi ne na karshe na majalisar a wannan karo.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China