in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da cikakken taro na 4 na taron shekara-shekara na NPC
2012-03-12 16:28:34 cri

A ranar 11 ga wannan wata da yamma a dakin babban taron jama'a, aka bude cikakken taro na 4 na shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC, inda aka saurari da duba rahoton da kotun koli da hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin suka yi.

Shugaban kasar Sin Hu Jintao, Shugaban zaunannen kwamitin NPC Wu Bangguo, firaministan kasar Wen Jiabao da dai sauran shugabannin kasar sun halarci taron.

Shugaban kotun koli ta jama'ar kasar Sin Wang Shengjun ya takaita ayyukan da kotun ta yi a shekarar bara. Kuma game da ayyukan da za a yi a shekarar 2012, Wang Shengjun ya bayyana cewa, kamata ya yi a rika hukunci bisa dokoki don tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin. Kana ya kamata a dora muhimmanci kan inganta kwarewar ma'aikatan kotun wajen aiki.

Shugaban hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin Cao Jianming ya bayyana cewa, a bara hukumomin bin bahasi sun kara yaki da laifuffuka na fannin tattalin arziki, da kuma tabbatar da ikon mallakar ilmi, makamashi da kuma kiyaye muhalli, kana da kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tare da yaki da manyan laifuffuka.

Ban da wannan kuma, Cao Jianming ya bayyana cewa, a shekarar 2012 hukumomin bin bahasa na kasar za su kara yin bincike da magance aikata laifuffuka ta hanyar amfani da mukaminsu, da kara sa ido kan ayyukan daukaka kara, da inganta kwarewar ma'aikatan hukumomin, da kuma amincewa da aikin sa ido daga majalisar wakilan jama'a, da kuma zamantakewar al'umma.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China