in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na kasashen waje sun tattauna matakan canja salon raya tattalin arziki da Sin za ta dauka
2012-03-10 21:49:59 cri

Yayin da aka shirya taruka biyu a kasar Sin, kasashen duniya sun mai da hankali sosai game da wadannan tarukan da ake yi a kasar Sin. A cikin rahoton aikin gwamnatin Sin da firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a gun taron, Sin ta rage burin karuwar tattalin arziki a karo na farko zuwa kashi 7.5 cikin 100 cikin shekaru 8 da suka gabata, kuma ta jaddada sanya karfi wajen fadada bukatun sayayya, da gaggauta kafa tsarin yalwata sayayya cikin dogon lokaci, kuma abin da ya jawo hankalin jami'an gwamnatoci da 'yan kasuwa na kasashen waje, haka kuma kafofin yada labaru na kasashen waje sun bayar da sharhi cikin muhimman shafunansu.

Jaridar Wall Street ta yi bayani cewa, kasar Sin za ta rage yawan karuwar tattalin arziki zuwa kashi 7.5 cikin 100, wannan matakin da Sin za ta dauka ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta sa kaimi ga raya tattalin arziki a karkashin gwamnatin kasar ba, kuma za ta canja salon bunkasuwar tattalin arziki, don fadada bukatun sayayya a gida.

Haka kuma, kamfanin dillancin labaru na Bloomberg ya bayyana cewa, Sin ta tsara burin karuwar tattalin arziki da yawansa zai kai kashi 7.5 cikin 100, abin da ya nuna cewa, Sin ta karkata hankali daga saurin karuwar tattalin arziki zuwa kyautata ingancin tattalin arziki, da kara samar da moriya ga al'umma.

Ban da wannan kuma, jaridar Al-Ahram ta kasar Masar, wadda ke samun karbuwa a yankin Gabas ta tsakiya, da kamfanin dillancin labaru na yankin Gabas ta tsakiya sun mai da hankali game da tarukan biyu da ake yi a kasar Sin, kuma suna fatan koyon fasahohin da Sin ta samu wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma, yayin da ake samun yanayin tangal-tangal din a yankunan yammacin Asiya da arewacin kasashen Afrika, don samun lalubo bakin zaren warware rikici da matsin lamba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China