in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na tafiyar da gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya yadda ya kamata
2012-03-10 17:24:33 cri

Wakilinmu ya samu labari daga taron manema labarai da aka kira yau Asabar 10 ga wata da safe a cibiyar ba da labaran manyan taruka biyu da a halin yanzu ake yi a nan birnin Beijing, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya a shekarar 2009, an yi ta inganta matakan kiwon lafiya ga manoma, mazauna birane da garuruwa da kuma ma'aikatan birane, kuma mutanen da matakan ke shafa ma sai dinga karuwa suka yi, bayan haka, an kuma kyautata aikin kiwon lafiya ga al'umma

Baya ga haka, 'yan majalisar ba da shawarwari ga harkokin siyasa ta kasar Sin da suka halarci taron sun kuma ba da ra'ayoyinsu kan yadda za a yi gyare-gyare ga asibitoci mallakar gwamnati, da kuma shigar da jarin masu zaman kansu cikin fannonin da suka shafi kiwon lafiya da sauransu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China