in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a dauki hakikanin matakai don gudanar da ayyukan yin gyare-gyare da samun bunkasuwa a jihar Tibet na kasar Sin
2012-03-09 20:56:32 cri

A ranar 9 ga wata, shugabannin kasar Sin Hu Jintao, Wen Jiabao, Li Changchun, Xi Jinping, Li Keqiang, da He Guoqiang sun halarci shawarwari na tawagogin taron cikakken zama na 5 na majalisar wakilan jama'a a karo na 11.

Sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar har ila yau shugaban kwamitin soji na Sin Mr. Hu Jintao ya halarci shawarwari na tawagar jihar Tibet, kuma ya jaddada cewa, kamata ya yi a nace ga manufar da kwamitin tsakiya ta tsara wajen gudanar da aiki a jihar Tibet, da samun bunkasuwa ta hanyar da ke da yanayi na musamman na jihar Tibet da na kasar Sin, haka kuma a dauki hakikanin matakai don gudanar da ayyukan yin gyare-gyare da samun bunkasuwa a jihar Tibet. Ban da wannan kuma, inji shugaba Hu Jintao, wajibi ne a ci gaba da inganta salon samun bunkasuwa, da sanya karfi wajen tabbatar da zaman rayuwar al'umma, da saka kudi wajen kyautata zaman rayuwar al'umma, tare da daukaka matsayin aikin ba da hidima, don a sa jama'an kabilu daban daban su iya samun moriya bisa sakamakon da aka samu wajen yin gyare-gyare da samun bunkasuwa, har ma da kokartawa wajen kiyaye muhalli da tabbatar da kwanciyar hankali da zama cikin jituwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China