in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tilas ne a bi hanyar da ta dace da halin da ake ciki a kasar Sin yayin kokarin samun bunkasa
2012-03-09 17:06:23 cri

A ranar 9 ga wannan wata, a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya yi wani jawabi, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi a yi la'akari da halin da ake ciki a kasar Sin, ta haka ne za a iya bunkasa kasar. Kana ana bukatar kokarin da dukkan jama'ar kasar suke yi, da kuma bin hanyar da ta dace da halin da kasar ke ciki a yayin da ake kokarin samun bunkasa.

Wu Bangguo ya ce, tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, tsari ne mai tushe irin na siyasa a kasar. Kuma tsari ne na gurguzu na musamman mai alamar kasar Sin, dake kunshe da tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar. Wanan tsari shi ne tsarin tushe dake tabbatar da samun bunkasuwar kasar. Sabo da haka, tilas ne a tsaya tsayin daka kan wannan tsari.

Bugu da kari, Wu Bangguo ya bayyana cewa, a bana za a kara kyautata aikin tsara dokoki da tsarin dokoki iri na gurguzu wanda ya dace da kasar Sin ,don sa kaimi ga samun bunkasuwar fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Kamata ya yi, a shirya ayyukan tsara dokoki da kuma gudanar da ayyukan yadda ya kamata.

Wu Bangguo ya nuna cewa, a bana za a sa kaimi ga tsara dokoki a fannonin zamantakewar al'umma, tattalin arziki da kuma kyautata dokoki a fannin al'adu.

Bisa labarin da aka bayar, a shekarar da ta gabata, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya duba daftarin dokoki 24,ya kuma gyara wasu muhimman dokoki dangane da biyan haraji, yaki da cututtuka domin gudanar da aiki, da dai sauransu. Kuma an riga an mika daftarin dokoki da ya shafi aikin hukunta manyan laifuffuka don a dudduba shi a gun wannan babban taron wakilan jama'ar kasar.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China