in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rubuta tunanin nuna biyayya da kiyaye hakkin bil adam cikin dokar shari'ar laifuffuka ta kasar Sin
2012-03-09 15:44:49 cri

A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana kokarin bautawa jama'ar kasar tare da kiyaye babbar moriyarsu. A shekarar 1991, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayar da wani rahoton game da halin kiyaye hakkin bil adam da kasar Sin ke ciki, inda a karo na farko aka waiwayi sakamakon da kasar Sin ta samu a wannan fanni tare da nuna wa kasa da kasa halin da take ciki wajen kiyaye hakkin bil adam. A shekarar 1997, a yayin babban taron wakilan kasar Sin na 15 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an sake rubuta tunanin hakkin bil adam a cikin rahoton siyasa na wannan taron.

Game da wannan, wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakiyar shugaban cibiyar nazarin ilimin zamantakewar al'umma da kimiyya ta kasar Sin wadda take halartar taron da aka saba yi sau daya a ko wace shekara Wu Yin ta bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban cigaba wajen kiyaye hakkin bil adam sakamakon bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Wu Yin ta ce,  "Kasar Sin tana kokarin bunkasa sha'anin kiyaye hakkin bil adam bisa matakai daban daban sannu a hankali tare da yalwatuwar tattalin arziki, ya kamata a ciyar da aikin gaba bisa daguwar matsayin zaman rayuwar jama'ar kasa."

A karni na 21, sha'anin kiyaye hakkin bil adam a kasar Sin ya shiga wani sabon mataki, kuma aka rubuta tunanin "nuna biyayya da kiyaye hakkin bil adam" a cikin tsarin mulkin kasa a shekarar 2004, ya zuwa shekarar 2007, aka rubuta tunanin a cikin dokar mallakar kayayyaki ta kasar Sin. Yanzu, wato a shekarar bana, za a rubuta shi a cikin dokar shari'ar laifuffuka, hakan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin kiyaye rayuka, dukiyoyi da zaman walwala na jama'ar kasar yadda ya kamata, kuma a bayyane ne an gano cewa, tsarin dokoki wajen kiyaye hakkin bil adam a kasar Sin yana samun kyautatuwa a kai a kai. Game da wannan, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakin shugaban jami'ar jama'ar kasar Sin Wang Liming wanda ke nazarin dokokin kasar Sin cikin dogon lokaci ya nuna cewa,  "Tun daga karni na 19, aka fara kiyaye hakkin bil adam a fannoni uku wato dukiyoyi, rayuka da zaman walwala, a dalilin haka, gwamnatin kasar Sin ta himmantu kan wannan. Dokar mallakar dukiyoyin da aka zartas a shekarar 2007 ta kiyaye dukiyoyin jama'ar kasar Sin yadda ya kamata. Yanzu, an gyara dokar shari'ar laifuffuka domin kara kiyaye hakkin rayuka da zaman walwala na jama'ar kasar Sin."

An zartas da dokar shari'ar laifuffuka a kasar Sin a shekarar 1997, kuma wannan karo na biyu ne da aka yi gyare-gyare a kanta. A shekarar bana, aka kara rubuta abubuwa da yawa a ciki har zuwa kudurori digogi 65, ban da wannan kuma, an yi gyare-gyare kan wasu fannonin da yawansu ya kai 110. A ciki, abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne a rubuta tunanin nuna biyayya da kiyaye hakkin bil adam a ciki, inda aka tanada cewa, bai kamata ba a tilasta kowane mutumin kasar Sin da ya yarda da laifinsa tare da kiyaye zaman walwala na kowanensu.

Duk da haka, kasar Sin tana da yawan mutane kusan biliyan daya da miliyan dari uku, kuma ba ta samu bunkasuwa daga duk fannoni ba tukuna, shi ya sa, kasar Sin tana fuskantar kalubale da dama wajen kiyaye hakkin bil adam. Dole ne gwamnatin kasar Sin ta kara himma kan aikin tare da daukar matakan da suka wajaba domin sa kaimi kan aikin tabbatar da adalci da zaman jituwa a kasar, hakan shi ma zai taimaka wajen ciyar da sha'anin kiyaye hakkin bil adam gaba a kasar. Kan wannan batu, mataimakin direktan cibiyar nazari kan hakkin bil adam ta kasar Sin Liu Huawen ya nuna cewa,  "Bisa dokar kasa da kasa, dole a kiyaye hakkin bil adam, kuma dole ne a kara nuna kwazo da himma kan aikin domin cimma burin a duk duniya gaba daya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China